MIGAS
Akwai wani sabuwar nasara cikin kaya iri-iri na IFAM wanda ya k’ara girma kullum. Za ta yi wa k’aura babban sauyi ma k’aurar ta manyan tekuna.
Mun yi murna sosai da muna da alfahari saboda mu iya gabatar da ta yanzu:
JIRGIN K’ARK’ASHIN RUWA NA MIGAS
Lalle, wannan abu zai rage nisan Turai mai yawa!!!
*
Shi ne dace musamman na bukatar shigowan Turai ta teku! An yi wannan jirgi musamman na mak’asudin mak’etarar mashigin teku na Gibraltar. In an tuk’a a hankali mak’etara ya dad’e misalin awa shida.
*
Tun da ka fara tafiyarka wajen mak’asudinka Turai za ka ji ma’anar ‘yancin kai! Ba wanda zai yi caji $2000 da zai sa ka cikin wani b’awon k’waya mai iyo inda ka fuskanta ko k’arfin iska da teku ko k’arfin siyasar wariya na k’asa! Maimakon haka za ka yanke shawarar saurin tafiyarka a kanka!
*
Rabon iskar shak’a shi ne 21% da girma shi ne 2,4 m³, shi ya sa cewa iska zai isa awa 8-10. Bayan wannan kuma an iya kawo sabon iska da k’arin bututu wanda an iya saya ban da jirgi. Kamfas da taswira wadda IFAM ya yi za su taimake ka ka same hanya da ka isa mak’asudinka ba shakka! In ka tafi k’ark’ashin tsagin ruwa sai kad’an ruwan wanda ya kewaye ka yana da yawan zafi mai jin dad’i na 15°C da kuma saboda shiru za ka ji dad’in tafiya da gaske. Saboda jirgi mai buzuzu ne ba Guardia Civil zai iya same ka, ko da suke da kayan aiki na zamani wannan jirgi ba da alama kamar girmarsa ya fi girmar kifi sai kad’an. Kana da rashin had’ari da kyamara mai samun zafi na jan infira da mai samun amsa kuwwa da rada da sauransu! Wallahi! Kana da iyakar tsaro wadda ya kare ka da matakan shisshigi na gwamnati!!
*
A halin yanzu sai an iya samun sigar d’aya tak amma saboda haka kud’insa mai ban mamaki shi ne $150 kawai!
Fakitin tushe yana k’unsa dukan yankunan jirgi da ja-gora na harsuna da dama. Bayan wannan kuma akwai wani faifai bidiyo da cikakken nunin filla-filla. Ka iya hab’aka wannan fakitin tushe da tarawa dabam. Don akwai daman had’uwar dabam-dabam da rangwamen kud’i na musamman kowa zai sami samfur d’insa na daidai ba shakka!!

MAI MUHIMMANCI:
Kowane fakiti ya k’unshi ashane mai hana ruwa da mai kad’an: DON ALLAH KA YI HANKALI DA HALAKAR MIGAS D’INKA BAYAN ISOWARKA RAIRAYIN BAKIN TEKU!!